Yadda za ka sauke bidiyo daga Facebook da YouTube zuwa wayar ka

0
140

Ma’abota amfani da soshiyal Midiya, musamman Facebook da YouTube wasu ba sa iya sauke bideo din da suka kalla a Facebook din ko kuma YouTube a wayoyinsu. Kuma ga shi yanzu ana dora bideo masu yawa a wadannan kafafe ga kuma ‘series film’ (fim mai dogon zango) da ake gabatarwa kusan kullum.

Yadda Za Ka Sauke Bideo Daga Facebook

Idan kana so ka sauke bideo daga Facebook a wayarka, to ka tabbatar a wayar ta ka akwai manhajar Dender. Idan ka ga bideo din da kake so ka sauke daga Facebook, to akwai hanyoyi guda biyu da ake bi. Hanyar farko shi ne, idan ka ga bideo din da kake so ka sauke din, sai ka duba saman bideo din, ta santar sunan wanda ya dora bideo din, bangaren dama, za ka ga wasu digo guda uku, kamar haka … To sai ka taba wadannan digo guda ukun (option kenan). Idan ka taba, zai nuno maka wasu rubututtuka a jere, sai ka duba za ka ga ‘Copy Link’ sai ka taba shi. Idan ka taba shi, ka yi kwafi din bideo din kenan, sai ka tafi inda za ka sauke shi, wato dender kenan. Sai ka je ka bude dender dinka. Idan ka bude dender din, a can kasa za ka ga rubututtuka, to za ka ga social, sai ka taba shi. Idan ka taba shi, zai nuno maka wasu rubutu a sama kamar haka; Status, Facebook, Instagram, Tiktok. To sai ka taba Facebook din. Wani dender din kuma zai nuno maka ‘paste and download’ sai ka taba shi kawai, za ka ga bideo din ya fara sauka.

Idan ka taba Facebook din, zai nuno maka wani waje an rubuta ‘paste Facebook link here’ wato ka ajiye link din da ka yi kwafi a nan. Sai ka danne yatsanka na dan wasu sakanni a wajen da aka rubuta ‘Paste Facebook Link here’ Za ka ga ya nuno ‘Paste’ sai ka taba wannan paste din. Kana taba wannan paste din, to wannan kwafi din da ka yi na bideo din zai sauka a wajen. To a kasan wannan waje, za ka ga wani koren rubutu, an rubuta paste & download. Sai ka taba shi, to za ka ga bideo din ya sauka. Sai ka dan jira kadan, za ka ga ya sauka.

Wannan yadda ake sauke bidiyo ta Xender kenan.

Hanya ta biyu kuma da ake bi wajen sauke bideo daga Facebook shi ne, ta hanyar Facebook Bideo downloader. Za ka je play store ka nemi manhajar ‘Fb bideo downloder’ zai nuno maka su da yawa, sai ka zabi daya daga cikinsu. Sai ka sauke shi akan wayarka. Idan ka sauke shi, sai ka bude shi, zai nuno ka saka Email ko lambar waya da password din da ka bude Facebook dinka da shi. Idan ka saka, za ka ga Facebook dinka ya hau. To shi a cikin wannan Facebook bideo downloader din, duk bideo din da ka gani kana so ka sauke, to a tsakiyar bideo din za ka ga alamar play, sai ka taba shi, zai nuno maka abubuwa guda uku, kamar haka; Cancel, Watch, Download. To kana taba download zai fara sauka a wayarka. Idan ka dan jira kadan zai sauka a wayarka duka.

Yadda Ake Sauke Bideo Daga Youtube

Da yawan mutane suna koka wa akan ba sa iya sauke bideo akan wayarsu daga manhajar YouTube. To idan kana so ka sauke bideo daga YouTube, sai ka je play store ka sauke manhajar Bidmate a kan wayarka. Idan ka sauke shi, sai ka bude shi, to zai nuno maka WhatsApp, Facebook, YouTube da sauransu. Sai ka taba kan YouTube din, zai bude, zai nuno maka wasu bideos din.

To a sama akwai wajen nema (searching), sai ka rubuta sunan bideo din da kake nema din. Idan ka taba wajen nema din, to zai nuno maka bideo din da kake nema. Idan ya nuno maka, sai ka taba kansa, ta ke zai fara magana. To a kasa, za ka ga wani arrow ja. Idan kana so ka sauke bideo din a kan wayarka sai ka taba wannan bideo din. Kana taba shi, take zai fara sauka a kan wayarka. Cikin sakanni, zai sauka akan wayarka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here