Sojoji sun Kashe ‘yan bindiga da dama sun tarwatsa sansanin su a Kaduna

0
129

Dakarun ‘Operation Forest Sanity’ sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da tarwatasa sansaninsu a karamar hukumar Chikun da ke Jihar kdauna.

Wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Tsaron Cikin Gidan jihar, Samuel Aruwan, ya fitar, ta ce dakarun sun samu wannan nasarar ne, biyo bayan fafatawa da dakarun suka yi yayin da suke yin sintiri daura da dajin Kaboresha zuwa Rijana da ke a yankin Kuzo-Kujeni-Gwanto a karamar hukumar Kachia.

Sanarwar ta kara da cewa, dakarun sun kuma tarwatsa sansanan ‘yan bindiga guda takwas da ke a Kutura zuwa Rijan, inda hakan ya sa wasun suka tsere.

Dakrun sun kuma kwato babura uku da wasu kaya da dama ciki har da kakin sojoji daga hannun ‘yan bindigar.

Sanarwar, ta ce gwaman jihar, Nasir El-Rufai, ya yaba da kokarin dakarun suka yi kan wannan nasarar suka samu.