Mutane 67 sun mutu a wani hatsarin jirgin sama a Nepal

0
106

Akalla mutane 67 ne aka tabbatar sun mutu bayan da wani jirgin saman fasinja mai dauke da mutane 72 ya yi hatsari a Nepal a safiyar Lahadin nan, hasarin jirgin sama mafi muni a kasar a cikin shekaru 30.

Bayanai sun ce jirgin ya fadi ne a tsakanin tsohon da sabon filin tashi da saukar jiragen sama na Pokhara da ke tsakiyar kasar ta Nepal, kuma nan take ya kama da wuta, yayin da har yanzu jami’an bada gaji ke aikin su.

Wani kakakin sojin Nepal ya tabbatar da cewa an garzaya da gawarwaki 29 asibiti, kuma akwai guda 33 a  inda lamarin ya auku a Pokhara da ke tsakiyar kasar.

Wani jami’in yankin ya ce akwai wadanda suka tsira, kuma an kai su asibiti, sai dai babu wani tabbaci a kan haka daga hukumar kamfanin sufurin jiragen sama na Yeti.

Kakakin kamfanin sufurin jiragen sama na Yeti, Sudarshan Bartaula ya ce daga cikin fasinjojin jirgin akwai ‘yan kasashen waje 15 da suka hada da Indiyawa 5 da wasu ‘yan kasar Rasha 4 da ‘yan Korea 2.

Jirgin saman da ya tashi daga birnin Kathmandu ya rikito ne a cikin wani kwarin tsaunuka, ya kuma wargaje a kusa da sabon filin tashi da saukar jiragen sama na Pokhara.