Jami’an tsaro sun kubutar da fasinjojin jirgin kasan Edo 12

0
135

Hukumomin jihar Edo ta ce an kuɓutar da fasinjoji 12 na jirgin ƙasa, da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a tashar jiragen ƙasa da ke jihar a makon da ya gabata.

An kama wasu daga cikin ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su, to sai dai wasu daga cikinsu sun tsere tare da wasu fasinjojin biyu a lokacin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin kuɓutar da su.

Hukumomin jihar sun ce an kuɓutar da mutanen 12 a lokacin da jami’an tsaro suka yi wa masu garkuwa da mutanen kwanton ɓauta.

Tuni aka kai mutanen da aka kuɓutar ɗin asibiti domin duba lafiyarsu.

Gwamnatin jihar ta alƙawarta ci gaba da nemo sauran fasinjojin biyu da ke hannun ‘yan bindigar.

Gwamnan jihar ya soki hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta ƙasar kan gaza samar da tsaro kan tasoshin jiragen ƙasan duk da faruwar makamancin wannan hari a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar a shekarar da ta gabata.

Tun da farko dai hukumomin sun ce mutum 32 ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su a harin da suka kai tashar jirgin ƙasa ta Igueben a makon da ya gabata, to sai dai daga baya hukumomin sun ce adadin mutanen 20 ne.

An saki mutum shida a farkon makon nan a wani samame da jami’an tsaro suka kai wa ‘yan bindigar.

Kama mutane domin neman kuɗin fansa ba sabon abu ba ne a Najeriya, lamarin da ya zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen tsaro a ƙasar a ‘yan shekarun baya-bayan nan.