Kotu ta wanke Benjamin Mendy daga zargin yiwa mata 4 fyade

0
127

Kotu a Ingila ta wanke dan wasan Manchester City Benjamin Mendy daga zargin aikata fyade kan Mata 4 da aka shafe fiye da watanni 6 ana shari’a akai.

Mendy dan Faransa mai shekaru 28 da ya lashe kofin Duniya a shekarar 2018 ya rufe fuska da hannayensa biyu cikin tsananin farin ciki lokacin da Alkali ke sanar da hukuncin a dakin sauraron kara na Chester Crown.

Rahotanni sun ce tun a larabar da ta gabata aka kammala yanke hukunci kan kararrrakin amma ba a kai ga bayyana hukuncin ga jama’a ba sai a jiya juma’a.

Zaman yanke hukuncin da ya kunshi alkalai 11 7 Maza da kuma 4 Mata ya tabbatar da cewa Mendy bai aikata dukkanin laifuka 6 da ake tuhumarsa ba da suka kunshi yiwa mata 4 fyade da kuma cin zarafin wasu ta hanyar lalata.

Duk da cewa kotun ta bukaci sake zaman shari’a kan wasu tuhume-tuhume 2 da ake yiwa Mendy amma ta tabbatar da cewa dan wasan na Manchester City bai aikata cin zarafi kan kananan matan 4 ba kamar yadda aka shafe watanni 6 ana tuhumarsa.   

Wannan zarge-zarge dai sun jefa dan wasan na Faransa a tsaka mai wuya bayan da ya fuskanci dakatarwa daga kungiyarsa Manchester City tun a watan Agustan shekarar 2021.