‘Yan bindiga sun tashi bom a shalkwatar karamar hukumar Ihiala a Anambra

0
126

A Najeriya, jami’an tsaron sa kai 3 sun mutu a jiya Alhamis, bayan da ‘yan bindiga suka tarwatsa shelkwatar karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra da ke yankin kudu maso gabashin kasar, ta wajen amfani da bama baman da aka kera a gida.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 2 na dare zuwa wayewar garin Alhamis, lokacin da ‘yan bindigar suka yi amfani bama bamai a shelkwatar karamar hukumar Ihialar, abin da ya lalata gine gine da dama a harabar.

Wasu majiyoyi daga karamar hukumar sun ce ‘yan bindigar sun fille kan daya daga cikin ‘yan sa kai 3 da suka kashe.

A wata sanarwa, kakakkin rundunar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce jami’an ‘yan sanda sun isa harabbar shelkwatar karamar hukumar da misalin karfe 3 saura minti 5 don kai dauki, inda ya ce an yi rashin sa’a, saboda a lokacin  maharan sun riga sun kashe ‘yan sa kan, har  ma sun fille kan daya daga cikinsu.

Ya kara da cewa biyar daga cikin gine ginen da ke sakatariyar sun kone kurmus sakamakon wannan harin, inda ya ce ‘yan sanda sun yi nasarar kashe daya daga cikin maharan, abin da ya takaita barnar da suka yi niyyar yi.

Jihar Anambra na daya daga cikin jihohin yankin kudu maso gabashin Najerya  da ke fama da hare haren ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan kungiyar IPOB masu fafutukar neman kasar Biafra ne.