Faransa za ta karbi aron akwatin gawar Fir’auna don bajekolinta ga jama’a

0
217

Mahukuntan Masar sun sanar da shirin baiwa Faransa aron akwatin gawar Fir’auna wato Pharoah Ramses na 2 wadda a karon farko za ta koma kasar bayan karbo ta shekaru 50 da suka gabata.

A ranar 7 ga watan Aprilun shekarar nan ne za a kai akwatin gawar ta Fir’auna dakin nuna kayakin tarihi da ke birnin Paris a Faransa wadda za ta kai har ranar 6 ga watan Satumba gabanin shafe tsawon watanni a gidan.

Ana saran akwatin gawar ta Fir’auna ta ja hankalin tarin masu yawan bude ido lura da yadda za a gudanar da bajekoli na musamman don nuna akwatin mai dogon tariohi ga wadanda ke fatan ganinta tsawon lokaci.

Guda cikin masu bincike kan kayakin tarihin masarautar Masar Dominique Farout ya bayyana farin cikin zuwan gawar Paris yana mai cewa sai da ya yi kwalla da ya san batun kawo gawar Paris domin kuwa lokacin da aka dauke ta daga kasar a shekarar 1976 bai wuce shekaru 16 a duniya ba.

Bayan barinta Faransa, gawar za ta yada zango a Sydney da San Francisco inda a nan ma jama’a za su tattaru don ganewa idonsu.