Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 2, sun ceto mutane 30 da aka sace a tsakanin Abuja da Nassarawa

0
89

Rundunar hadin gwiwa ta ‘Guards Brigade da Civilian Joint Task Force’ (CJTF) sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da kubutar da mutane 30 da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai a yankin Idu, Chikara, da ke kan iyakar karamar hukumar Toto.

Iyakar da ke tsakanin Jihar Nasarawa da Abaji a Babban Birnin Tarayya, Abuja da Koton Karfe a Jihar Kogi.

Wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Kyaftin Godfrey Abaakpa ya fitar, ta ce bataliya ta 177 ne suka gudanar da wannan samame tare da dakarun ‘Operation Wild Stroke da CJTF’ a matsayin wani shiri na dakile ta’adanci.

Ya ce yayin aikin hadin gwiwa, sojojin sun fatattaki ‘yan bindigar tare da kashe biyu daga cikinsu yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Sojojin sun kuma ceto wasu mutum 30 da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su, inda ya kara wani jami’i day ya samu rauni kuma a halin yanzu yana cikin kwanciyar hankali kuma yana samun kulawar da ta dace a asibiti.