Ana zargin wani mutum da yi wa wata mata fyade a gaban ‘yarta

0
128

Jami’an tsaro farin kaya (NSCDC) a Jihar Kwara, sun kama wani mai shekara 47 da ake zargi da yi wa wata mata fyade a gaban ‘yarta mai shekaru biyu kacal a duniya.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar jihar, Olasunkanmi Ayeni, ya fitar, ta ce wanda ake zargin ya aikata fasadin ne a yankin Oloje da ke a garin Ilorin, babban birnin jihar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, bayan wanda akw zargin ya aikata wannan ta’asar, ya kuma sace wa matar kwamfuta da wayoyin hannu guda biyu.

A cewar sanarwar, an kawo rahoton aukuwar lamarin ga NSCDC a Jihar Kwara a ranar 1 ga watan Janairu 2022, inda hukumar ta bazama yin bincike har ta samu damar kamo wanda ake zargin a garin Mokwa da ke Jihar Neja a ranar 5 ga watan Janairu 2023.

Sanarwar ta kara da cewa, da rundunar ta gudanar da binciken a kan sa, wanda dan asalin ya Abeokuta da ke a Jihar Ogun, kuma ya amsa laifinsa.

A cewar sanarwar, wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar jajiberin shigowa sabuwar shekarar 2023 ta hanyar fasa rufin gidan matar da ke a Oloje, inda ya yi mata fyaden da karfi da yaji.

Sanarwar ta ce, da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da shi a gaban kotu.