2023: Shugaban INEC ya gana da shugabannin jam’iyyun siyasa a Abuja

0
115

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi wata ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa 18 a hedkwatar hukumar da ke Abuja.

Taron wanda shi ne na farko a bana, an yi shi ne don gabatar da rajistar masu kada kuri’a a shekarar 2023 ga jam’iyyu gabanin zabe kamar yadda dokar zabe ta 2022 ta bukata.

Wadanda suka halarci taron sun hada da shugabannin jam’iyyar APC da PDP da Labour Party LP, da NNPP da dai sauransu.