‘Yan sanda sun cafke matar da take yi wa ‘yan bindiga safarar bindigu a jihar Zamfara

0
130

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama wata mata mai safarar makamai ga ‘yan bindiga tare da takwaranta namiji a hanyar Gusau-Wanke-Dansadau dake jihar.

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Ya ce an kama wadanda ake zargin ne da harsashi 325 da kuma kwalbasar alburusai guda daya na bindigar AK-47.

Ya bayyana cewa kamen ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu game da safarar makaman daga jihar Benue zuwa wani sansanin ‘yan bindiga da ba a bayyana ba a Zamfara.