Yadda boka ya dirka wa wata mata ciki a Kano

0
121

Hukumar Hisbah a Jihar Kano, ta kama wani boka da ake zargi da yi wa wata mata ciki bayan ta je wajensa neman magani.

Bokan mazaunin karamar hukumar Dawakin Kudu an kama shi bayan matar da ba a bayyana sunanta ba, ta kai kara tana neman a bi mata hakki dauke da cikin wata bakwai.

Rahotanni sun nuna cewa Bokan ya yi fice wajen yaudarar mata, ciki har da matan aure.

Bokan na yaudarar mata ta hanyar shaida musu cewa idan suka kwana da shi zai ba su maganin da zai hana a yi musu kishiya da kuma samun damar mallakar miji.

Matar ta shaida wa Hisbah cewa lokacin da ta je neman maganin wajen Bokan, ya shaida mata cewa ba zai yiwu ba, sai sun kwana tare.

A cewarta, mutumin ya jima yana neman saduwa da ita, idan sun je wajen tare da mahaifiyarta, amma bai yi nasara ba har sai lokacin da ta ziyarce shi ita kadai.

Bokan, ya amsa wannan laifin, sai dai ya ce aikin shaidan ne.

Shugaban rundunar Hisbah reshen karamar hukumar, Ustaz Kabiru Musa Dawakiji, ya ce za su ci gaba da bincike domin daukan mataki.