Wani matashi ya kashe kishiyar mahaifiyar sa da ‘yarta a Kano

0
110

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta kama wani matashi dan shekara 20, Ghadaffi Sagir bisa zargin kashe kishiyar mahaifiyar sa malama Rabi da ‘yarta.

Kakakin rundunar, SP. Abdullahi Kiyawa ya tabbatarwa DAILY POST faruwar lamarin.

Ya ce lamarin ya faru ne a daren Asabar da misalin karfe 11:00 na dare a Rijiyar Zaki daura da Layin Dorawanyan Kifi a karamar hukumar Ungogo.

Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi amfani da wani makami mai kaifi, inda ya yanka Matar da ‘yarta wanda hakan yayi sanadin mutuwarsu har lahira.

Kiyawa ya ce an kama wanda ake zargin kuma ya amsa laifinsa.

Binciken da ‘yansandan suka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya kashe Malama Rabi ne bisa zarginta da haddasa rabuwa tsakanin mahaifiyarsa da mahaifinsa.

Wanda ake zargin, ya kashe ‘yar uwarsa, ‘yar Malama Rabi sabida ta ganshi sanda yake kashe mahaifiyarta.