Manhajojin da ke bata wayar Android ta hanyoyi da dama

0
112

Kamar yadda kowa ya sani wayar Android ana loda mata manhajoji (Applications) iri daban-daban. Idan aka ce ‘App’ wato (application) ko ‘Apk’ wato
(Android Package Kit) shi ne abubuwan da wayar Android take amfani da shi don saukake aiki da wayar wajen yin amfani da ita kai tsaye ga abin da kake so ka sarrafa a wayarka. Sannan applications ana saka su a waya har ma ana iya tura wa a wasu Android din.

Duk wayar Android tana bukatar manhajoji don tafiyar da ita cikin sauki, domin sune za su taimaka wa mai amfani da wayar wajen jin dadin amfani da ita.

Akwai Applications masu yawan gaske da mai Android zai iya amfani da su kamar irin na Banki, Chat, Music, Browsers, Game, da na Karatu da sauransu. Amma kuma bayan wadannan Apps din wadanda suke da matukar amfani ga mai wayar Android, sannan kuma akwai wadanda suke ba su da amfani sosai, sai dai ma a ce cutar da wayar suke maimakon amfanarwa.

Ire-Iren wadannan Manhajojin masu cutarwa, iri biyu ne. Akwai masu cutarwa kaitsaye da kuma masu cutarwa a hankali-hankaliba tare da mai amfani da wayar ya sani ba. Irin wadannan sun hada

UC Browser-

UC Browser yana daya daga cikin shahararrun ‘applications’ da ake yawan amfani da su a wayar Android. Play store ya bayyana cewa an sauke (download) fiye da miliyan 500, dalili kuwa bai wuce saurin sauke abu da yake yi da wuri ba, da kuma ci gaba (acceleration) da yake da shi, da kuma kyakkyawan shafi mai tsari.

Bayan amfanin da yake da shi, akwai matsaloli kamar haka:

-Yana daukar bayanai kamar contacts, SMS da location.

-Ana tuhumarsu da sayar da bayanan sirri na mutanen da ke amfani da shi a wasu mutane a waje, kamar IMEL, IMSI da wasu bayanan ga kamfanin ALIBABA, ba tare da izinin mai wayar ba kuma babu tsaro (encryption).

To don haka kuwa bayananka za su fita waje zuwa ga wasu mutane da za su iya maka kutse (hacking), su sace password dinka ba tare da ka sani ba.

CLEAN MASTER:

Manhajar Clean Master akwai bayanai masu ba da mamaki, domin kuwa yana da ‘rebiews’ a play store wajen miliyan 43 (duk da akwai wasu kamfanonin Apps dake biyan kudi don su samu (rebiew) din.

Shi wannan applications din kamfaninsa ya yi alkawarin zai taimaka wa mai amfani da shi wajen goge abubuwan da ba su da amfani (junk files) a ma’adana (memory), da kuma da bawa waya damar samun sarari (space), da kuma karin sauri wajen shiga yanar gizo (Internet browsing).

Matsalar da ake samu da shi ba wani na damuwa ba ne sosai, sai dai duk ayyuka da yake yi sabbin wayoyin Android suna dauke da shi, ba ka bukatar sai ka saka application mai yin irin wannan aikin.

Idan kana bukatar goge ire-iren wadannan abubuwa marasa amfani, ka bi wadannan matakan daga wayarka;
Settings>Apps>Storage >Clear Cache… Shikenan ka samu lafiya.

Sannan kuma idan ka kunna datarka, zai rika fito da wasu shafuka (ads) wadanda ba ka da alaka da su, sai dai su cinye maka datar kuma su hana wayarka sauri wajen yin browsing, kuma yana adana wadannan bayanai a cikin wayarka a boyayyen waje ba tare da ka sani ba, a cikin ma’adanarka (memory).

Du Battery Saber

Du Battery Saber: tun wajen shekarar 2012 aka kirkiro wannan application din, kuma ya samu karbuwa sosai, domin an sauke shi (downloading)fiye da miliyan 100, daga play store.

Sannan kuma masu App din sun yi shi ne don ya taimaka wajen yin cajin Batirin waya da sauri (fast charging), da kuma sanya waya yin sauri (speed).

Amma wannan duk yaudara ce kawai, domin abubuwan da ke sanya waya saurin caji sune kamar haka:

-Ya zamanto wayarka tana goyon bayan caji da sauri (support fast charging)

-Amfani da caja mai sauri musamman wanda waya ta zo da shi.

Amma babu wani application da zai sa wayarka saurin yin caji.

Wata matsala kuma ita ce, wannan application din a kowane lokaci a bude yake, wanda hakan na jawo shanyewar cajin waya maimakon ragewa, kuma yana amfani da datar wayarka in dai a bude yake, wajen fito da shafukan da ba ka bukata (ads) da za su iya sa wayarka tana yin rashin sauri (slow).

Duk wasu applications da ke nuna za su taimaka maka wajen rage shan Batir, ko sa wayarka sauri (speed), ko rage fili (space) a ma’adana (memory), ba su da amfani, tun da an yi wayoyi masu rike caji sosan gaske.

ES FILE EXPLORER

Shi wannan application din, masu amfani da shi za su yi mamaki idan aka ce musu yana daga applications masu matsala. Ba don komai ba sai don amfaninsa ga mai wayar Android da kuma yadda mutane suka tasirantu da shi.

A wannan zamanin, sabbin wayoyi da ke fitowa sun zo da irin tsarin da wannan application din yake dauke da shi, ba ka da bukatarshi a yanzu, sai dai ya cike maka ma’adana (memory) kawai.

To shi ma yana da matsaloli kamar haka:

-Yana bullo da shafukan talla (ads) da kanshi

-Yana tura bayanai ga wasu wurare ba tare da izini ba, wanda hakan na ba da dama ga masu kutse (hackers) su shiga su maka barna a wayarka.

Idan har ka matsa da yin amfani da ‘file manager app’, to ka yi amfani da ‘FILE GO’ wanda kamfanin GOOGLE masu manhajar ANDROID suka kirkiro, ya fi inganci da kuma tsaro a wayarka.

ANTI VIRUS APPs

Kusan duk application da ke da tsarin anti birus suna da mantsaloli da yawa fiye da amfanarwa. Ga shi kuma mutum da zarar ya sayi waya, tunanin farko shi ne saka anti birus akan wayar, domin samun ingantaccen tsaro. Abin da mutane ba su sani ba shi ne tsarin manhajar Android (operating system) ya yi daban da tsarin manhajar (windows) na’ura mai kwakwalwa (computer).

Manhajar Android ba ta bukatar anti birus don samun kariya da kuma tsaro ga waya.

Kusan duk apps na anti birus sukan tambayi izini (permission), bayan an ba su, sukan samu cikakken dama (access) ga dukkan bayanai da ke cikin wayarka tun daga kan kira (calls), sakonni (messages), bayanan sauran apps din da ke wayarka, da passwords, da kuma duk wasu ajiyayyun fayil (file) a wayarka, kuma sukan tura irin wadannan bayanai ga wasu kamfanoni ba tare da izinin mai wayar ba.

Idan kana bukatar wayarka ta samu fili (space), kuma ta daina zafi (heat), da nauyi (delay) to ka kauracewa irin wadannan apps din na anti birus. Akwai application a Google Play store mai suna PLAY PROTECT FUNCTION, ka sauke shi, ka installing dinsa a wayarka, to za ka samu tsaro mai inganci, domin masu manhajar Android wato Google su suka kirkiro shi.