Alakar gwarzon dan kwallo Pele da Afirka

0
135

A ranar Talatar data gabata ne dai aka binne gawar shahararren dan wasan kwallon kafar nan na duniya, Pele, wanda ya mutu a ranar Alhamis ta satin da ya gabata yana da shekara 82 a duniya.

Dubban masu makoki ne suka hallara a filin wasan Santos na Brazil, domin ganawa da gawar tsohon dan wasan duniyar kuma an ajiye gawar Pele a tsakiyar filin Urbano Caldiera da ke Sao Paulo, yayin da magoya baya suka yi dogon layi suna tozali da ita.
Tsohon dan wasan wanda ya kafa tarihin cin kofin duniya sau uku a tarihi, ya mutu ne bayan ya sha fama da jinya wadda ya dade yanayi kuma a wasu lokuta a baya ma aka dinga yada jita-jitar cewa ya mutu.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci jana’izar akwai shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino, wanda ya ce za su bukaci kowace kasa a duniya ta saka sunan Pele a daya daga cikin filayenta.

Kasancewar Pele daya daga cikin manyan taurarin matasan bakaken fata a fagen wasanni a zamanin talabijin, Pelé ya samu karbuwa da kauna daga ‘yan Afirka a fadin nahiyar gaba daya.

A lokacin da kasashen Afirka ke fafutukar samun ‘yancin- kai a karshe-karshen shekarun 1950 da kuma farko-farkon shekarar 1960, Pelé ya dinga samun gayyata daga kasashen Afirka da suka samu ‘yanci, domin wasan sada zumunta da kungiyar sa ta Santos FC da kuma tawagar kasar sa ta Brazil.