Karamin yaro ya harbi malamar sa da bindiga a Amurka

0
120

Jami’an tsaro a Jihar Virginia ta Amurka, sun tabbatar da yadda wani dalibi mai shekaru shida a duniya, ya harbi malamarsa tare da ji mata mummunan rauni bayan ta ba ta masa rai a lokacin da ta ke ba su darasi a makaranta.

An rawaito cewar lamarin ya faru ne a ranar Juma’a.

Jaridun kasar sun rawaito cewa an yi nasarar ceto ran malamar ne bayan kai mata agajin gaggawa ko da ya ke har yanzu ta na dakin kula da marasa lafiyan da ke matsanancin hali.

Jami’an ‘yansandan jihar, sun tabbatar da faruwar lamarin sai dai ba su yi karin bayani kan dalilin da ya haddasa harbin malamar ba.

A cewar ‘yansandan, dalibin mai shekaru shida a duniya ya shiga makaranta da bindiga ne, kuma suna kan bincike don gano daga inda bindigar ta fito.