Sarkin Dakwa ya aurar da ‘yan mata 17 ga samari 17 gami da nadin sarautu

0
111

A safiyar ranar Asabar da ta gabata ce, Mai Martaba Sarkin Dakwa Dakta Alasan Baba Chikuri, ya aurar da samari da ‘yammata 34, maza 17 mata 17, an gabatar da bikin ne a fadar sarkin da ke Dakwa ta yankin Karamar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.

Bikin da ya samu halartar manyan baki daga sassan kasar nan.

Babban bako kuma uba a wurin shi ne, Tsohon Gwamnan Jihar Kano Kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, wanda kuma shi ya zama a matsayin uba ga ‘yammatan wanda shi ya ba da aurensu.

Wakilin LEADERSHIP Hausa Auwal Mu’azu, ya samu zantawa da Sanatan jim kadan bayan kammala daurin auren inda ya nuna godiya da farin cikinsa da zuwa wannan masarauta, musamman yadda ya ga an tsara gudanar da wannan aure. ” A yau wadannan mutum 34 za su kwana cikin farin ciki, da yawa mutane ba su gane fa’idar irin wannan aure a addinance ba, kuma basu gane shi a zamantakewa ba.

Yau sarki ya tuno min da wacan lokaci da muka yi auren maza da mata sama da dubbai, wanda yau din nan cikin yardar Allah.” In ji shi. Ya yi kira ga shugabanni da masu hannu da shuni da su yi koyi da irin wadannan abubuwan alheri.

A cewarsa wannan tsari ne da zai taimaka wa marasa hali su samu sukunin aurar da ‘ya’yansu, a karshe ya yi addu’ar fatan Allah ya sanya alheri ya kuma zaunar da su lafiya.
Tun da fari a nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Dakwa Dakta Alasan Baba Chikuri, godiya ya yi ga Allah bisa wannan rana mai mhimmanci, kazalika ya yi godiya ga jagoran na Kwankwasiyya bisa amsa gayyatarsa da ya yi, gami da yi masa fatan alheri da addu’ar Allah ya biya masa bukarsa na abubuwan da ya sa gaba.