‘Yan sanda sun cafke mutane 61 da ake zargi da bangar siyasa a Kano

0
128

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano a ranar Alhamis ta ce ta kama wasu mutane 61 da ake zargi ‘yan bangar siyasa ne a kokarinta na kawar da duk wani nau’in laifuffuka da yawo da muggan mukamai musamman a lokutan yakin neman zabe.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda, ​​ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya raba wa manema labarai a Kano.

A cewarsa, an yi kamen ne bisa umarnin babban sufeton ‘yan sanda na kasa, Usman Alkali-Baba, na tabbatar da an gudanar da zabe cikin lumana da kuma magance matsalar ‘yan bangar siyasa.

“An kama wadanda ake zargin ne ranar 4 ga watan Janairu, yayin da ake gudanar da yakin neman zaben APC da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha Kano,” in ji shi.

Ya ce abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wukake guda 33, kwalabe guda takwas, almakashi hudu da dai sauransu.