2023: Mai binciken kudin PDP da wasu jiga-jigan jam’iyyar sun koma NNPP a Gombe

0
114

Yayin da saura makonni takwas a yi zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya, kuma saura makonni goma a yi zaɓen gwamnoni, NNPP na ci gaba da samun tagomashi a Jihar Gombe.

Farkon wannan makon ne Babban Mai Binciken Kuɗin PDP na Jihar Gombe, Honorabul Mahmoud Mohammed Wafa ya fice daga jam’iyyar, ya koma NNPP.

Wafa ya bayyana ficewar ta sa ce a lokacin da ya kai wa ɗan takarar gwamnan Gombe na NNPP, Khamisu Mailantarki ziyara a gidan sa da ke Abuja.

Ya ce ya shiga NNPP ne domin a haɗa hannu dashi a ceto Jihar Gombe daga hannun gwamnatin APC, wadda ya ce ya ƙasƙantar da jihar Gombe a idon faɗin ƙasar nan baki ɗaya.

“Na shigo NNPP ne bisa la’akari da na yi cewa akwai buƙatar a haɗa hannu a ceto Jihar Gombe daga hannun APC. Sannan kuma ita PDP tun bayan zaɓen fidda gwani a shekarar da ta gabata ta samu gagarimar matsala. Saboda haka APC da PDP ɗin duk ba za su iya samar mana shugabanci na gari a Gombe ba.”

“Amma idan mu ka waiwaya baya dangane da tasirin da Mailantarki ya yi a baya, to shi ne zai samar da nagartaccen shugabancin da zai bunƙasa Gombe bayan zaɓen 2023.”

Tun da zaɓen 2023 ya gabato ne mambobi da wasu jiga-jigan APC da PDP ke da tururuwar ficewa su na komawa NNPP.

Ko a farkon wannan makon sai da wasu shugabannin PDP daga ƙananan hukimomin Funakaye da Dukku, su ka fice daga PDP su ka koma NNPP.