Rundunar sojin Najeriya ta zargi kungiyar IPOB da yin garkuwa da wata Laftanar

0
127

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa, daya daga cikin jami’anta, Laftanar PP Johnson, wanda wasu da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB/ESN ne suka yi garkuwa da ita a ranar Litinin 26 ga watan Disamba, 2022 a jihar Imo, yayin da ta ziyarci kakarta, har yanzu ba a sako ta ba sabanin rade-radin da ake yi.

Kamar dai yadda rundunar ta sha alwashin ba za ta bar wani abu ba a kokarinta na ceto jami’ar da kuma gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a, ya ce, “Rundunar sojin Najeriya na son bayyana cewa bayanan da suke yi ba su da tushe balle makama domin har yanzu ba a sako jami’ar ko kubutar da ita daga hannun wadanda suka sace ta ba.