Fitaccen dan wasan kwallon kafa Pele ya rasu

0
125

Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Brazil kuma wanda ya taba lashe kofin duniya sau uku Pele, ya rasu yana da shekaru 82 a duniya.

An yi la’akari da shi a matsayin fitaccen dan wasan kwallon kafa na farko a duniya.

Pele ya yi fama da ciwon daji na hanji, bayan tiyatar cire masa wani ciwon daji a watan Satumban 2021.

Kuma ya bukaci a yi masa magani akai-akai. Bayan an kwantar da shi a asibiti a karshen watan Nuwamba don sake nazarin maganin kansa.

An gano cewa yana da ciwon numfashi kafin daga bisani a koma da shi wurin kula da lafiyar jiki lokacin da jikinsa ya yi tsamari.