Obi ya zabi tsohon mataimakin Obasanjo, a matsayin wanda zai maye gurbin Okupe

0
104

Jam’iyyar Labour ta nada tsohon mai baiwa shugaban kasa Olusegun Obasanjo shawara kan harkokin siyasa, Mista Akin Osuntokun a matsayin sabon Darakta Janar na yakin neman zaben shugaban kasa.

Shugaban jam’iyyar na kasa Julious Abure ne ya bayyana hakan a Abuja, ranar Talata.

Ya ce an cimma matsayar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a fadin kasar.