Qatar 2022: Adadin kudin da kowacce kasa ta samu a gasar cin kofin duniya

0
164

Bayan kammala gasar cin kofin duniya a yammacin ranar Lahadi wanda Argentina ta doke kasar Faransa, hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta sanar da adadin kudaden da kowacce kasa ta samu tun daga wasannin cikin rukuni har zuwa wasan karshe.

Hakan na nufin baya ga kofin duniya da sarkar zinari da aka bai wa ‘yan wasa, Argentina za ta bar Katar da miliyoyin daloli saboda a bana hukumar kwallon kafa ta duniya ta ware kudin da za a ci kyauta da yawansu ya kai dala miliyan 440.

Kasashe 32 daga fadin duniya da suka wakilci nahiyoyinsu za su bar Katar da akalla dala miliyan tara kowannensu.

Tuni FIFA ta fitar da abin da kowacce kasa za ta samu gwargwadon matakin da ta kai a gasar da kuma sauran kasashen da suka samu damar zuwa gasar amma suka gaza tsallake matakin rukuni za su koma gida ne da dala miliyan tara kowannensu.

Hakan na nufin kasashen Katar da Ecuador da Wales da Iran da Medico da Saudi Arabia da Denmark da Tunisia da Kanada da Belgium da Germany da Costa Rica da Serbia da Kamaru da Ghana da da kuma Uruguay sun samu dala miliyan tara kowannensu.

Sai kuma kasashen da suka samu kai wa zagayen ‘yan 16, amma gudunsu ya kare daga nan da suka hada da Amurka da Senegal da Australia da Poland da Sifaniya da Japan da Switzerland da kuma Koriya ta Kudu, kowannensu ya samu dala miliyan 13.

Sannan wadanda suka samu kansu a zagayen kuarter-finals da suka hada da Brazil da Netherlands da Portugal da kuma England sun samu dala miliyan 17 kowannensu kamar yadda FIFA ta bayyana.

A fagen neman na uku kuwa, ma’ana gurbin da Maroko da Croatia suka samu kansu bayan kai wa zagayen kusa da karshe, Croatia ta samu dala miliyan 27, yayin da Maroko ta koma gida da dala miliyan 25 a matsayin na hudu.

Sai kuma zagayen karshe da aka warewa dala miliyan 72, Faransa da ta yi rashin nasara ita ce mai dala miliyan 30, yayin da Argentina da ta lashe kofi za ta koma gida da dala miliyan 42.

Har ila yau, FIFA ta kara yawan kudin da za a ci idan aka kwatanta da wasannin baya da dala miliyan 40, domin a shekarar 2018 kasashen da suka samu halartar gasar sun raba dala miliyan 400 ne.

Kafin 2006 kasashen da suka lashe gasar kofin duniya ba su taba wuce karbar sama da dala miliyan 10 ba, sannan Italiya ma da ta lashe kofin duniya a shekarar 1982 dala miliyan 2.2 kawai ta samu.

Ta ina Kudaden Suke Fitowa?

Tambayar cewa a ina hukumar kwallon kafa ke samun kudade tana da saukin amsawa, ta hanyar shirya gasa domin a gasar kofin duniya ta 2018 kawai, FIFA ta samu sama da dala biliyan 4.6 na kudin shiga.

Kuma kusan duk shekara hukumar ba ta rasa wata gasa da za ta shirya, duk da ba lalle ta samu makudan kudade ba kamar a gasar kofin duniya ta maza ba, sai dai a shekarar 2021 ne ma da ba ta shirya gasa ba, amma duk da haka sai da FIFA ta samu dala miliyan 766.

Mafi yawan ribar da FIFA ke samu na fitowa ne ta hanyar kudaden da ake biyanta wajen samun damar nuna wasannin kofin duniya da sauran gasa daban-daban da take shiryawa kuma gasar kofin duniya ce gasar da aka fi kallo a duk duniya, inda aka yi hasashen biliyoyi sun kalli gasar Katar 2022.

A gasar kofin duniya ta wadda Rasha ta karbi bakunci, sama da mutum biliyan hudu ne suka kalli wasan ta talabijin da sauran kafofin sadarwa na zamani. Haka kuma FIFA na karbar makudan kudade ga kamfanoni da ke tallar hajojinsu a lokacin da gasa ke gudana.

Tun kafin fara gasar cin kofin duniya na 2018, FIFA ta samu kusan dala biliyan biyu daga kamfanonin da ke son FIFA ta yi musu talla a gasar, sannan wasu kamfanoni kamar na gyam na bidiyo da ya shafi kwallon kafa na biyan FIFA makudan kudade domin amfani da sunanta, kuma kamfanin gyam din bidiyo na EASPORTS da ke Amurka ya bai wa FIFA dala biliyan 20 don amfani da sunanta a tsawon shekaru 20.

Wata hanyar kuma da FIFA ke samun kudin shiga ita ce sayar da tikitin shiga kallon wasanni, domin kusan tikiti miliyan uku FIFA ta sayar ga wadanda ke son kallon gasar Katar 2022 da aka kammala kuma farashin tikitin na farawa ne daga dala 100 zuwa dala 1,100.

Saboda haka ko a tikiti kawai FIFA na samun biliyoyin daloli na kudin shiga.

LEADERSHIP