Ba mu san adadin sabbin kudin da muka buga ba – CBN

0
176

Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ke kula da daidaita al’amuran kudi, Aisha Ahmad, ta ce ba ta san yawan adadin sabbin kudin da bankin ya fitar ba don fara amfani da su ba.

Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke amsa tambayoyi, a lokacin da ta bayyana a gaban majalisar wakilan dokokin kasar nan, don yi musu karin bayani kan tsarin takaita cire kudi da bankin ya samar.

A yayin da ake mata tambayoyi daya daga cikin ‘yan majalisar, Sada Soli, ya nuna damuwarsa dagane da karancin sabbin kudin, kwanaki kadan da sakin kudin don al’umma su fara amfani da su.

Sai dai mataimakiyar gwamnan, ta ce ba ta san adadin da aka saka ba na sabon kudin ba.

A ranar Laraba ne majalisar wakilai ta bukaci mataimakiyar gwamnan CBN ta bayyana a gabanta a yau Alhamsi, biyo bayan tafiyar da gwamnan bankin, Godwin Emefeli ya yi waje don a duba lafiyarsa.

A satin da ya gabata ne majalisar ta aike wa da Emefiele sammacin bukatar ganinsa don ya mata cikakken bayani kan tsarin takaita cire kudi.

Lamarin da tun farko ta soki lamirinsa, inda ta ce mutanen karkara za su fuskanci kalubale mai tarin yawa.