Gobarar wutar lantarki ta kashe mutum 11 a Zariya

0
135

Mutum 11 sun rasu sakamakon gobara da ta wutar lantarki da talatainin dare a unguwar Gwargwaje da ke wajen garin Zariya a Jihar Kaduna.

Wani mazaunin yankin Gwargwaje ya ce matsalar da wutar lantarkin da aka kawo ne ta haddasa gobara a gidan wani makwabcinsa, ta kone gidan kurmus.

Aminiya ta gano cewa sama da mutum 10 suna kwance a asibitin Wusasa da na Kofar Gayam, sakamakon kunar da suka samu a gobarar ta da tashi da misalin karfe 1 na dare, kafin wayewar garin ranar Laraba.

Wakilinmu ya tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Kamfanin Wutar Lantarki na Kaduna, Abdulazeez Abdullahi, domin karin bayani, amma ya ce daga baya zai bayar a rubuce.

Shi ma Babban Jami’in Hukumar Kashe Gobara da ke Zariya, Umar Muhammad, da muka tuntube shi, ya nemi a ba shi lokaci domin tattara bayanai.