Hukumar Hisbah ta kama wasu matasa 19 yayin da suke taron daurin auren jinsi a Kano

0
131

Jami’an hukumar Hisbah reshen jihar Kano sun cafke wasu matasa 19 a wata shahararriyar cibiyar taron da suke gudanar da auren jinsi.

Matasan ‘yan kimanin shekaru ashirin da haihuwa an ce sun taru ne domin shaida daurin auren wasu da ake zargin ‘yan luwadi ne, Abba da Mujahid.

An tattaro cewa jami’an Hisbah da ke hedikwatar hukumar da ke Sharada, Kano, sun isa wurin kafin a fara daurin auren, don haka an kama mata 15 da maza 4.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Haruna Ibn Sina ya bayyana cewa an kama su ne bayan wani rahoto da wani Bature nagari ya bayar game da auren jinsi.

Ya kara da cewa ‘yan biyun da aka yi wa lakabi da ‘ango da amarya’, Abba da Mujahid sun tsere bayan isowar jami’an Hisbah a wurin daurin auren.

Sai dai Ibn Sina ya bayyana cewa mai shirya taron, Salma Usman mai shekaru 21 a duniya a halin yanzu tana hannunsu, ya kara da cewa hukumar za ta kara zage damtse wajen ganin an cafke Abba da Mujahid.

Babban kwamandan ya ci gaba da cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano za ta mika wadanda ke hannunta zuwa ga ‘yan sanda domin daukar matakin da ya dace, saboda yawancin matan sun yi ikirarin cewa an gayyace su zuwa daurin auren ne daga wata jiha makwabta. Ya kuma nanata kudurin hukumar na kawar da duk wani nau’in munanan dabi’u a jihar.