Abun da Ronaldo ya fada bayan Messi ya lashe kofin duniya

0
134

Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Brazil, Ronaldo Luis Nazario de Lima ya taya Lionel Messi murnar nasarar da ya samu a gasar cin kofin duniya a Qatar, yayin da Argentina ta doke Faransa a ranar Lahadi.

Messi ya taka rawar gani mai ban mamaki a wasan da ya zura kwallaye shida a raga wanda aka tashi 3-3 bayan karin lokaci inda dan wasan Faransa Kylian Mbappe ya zura kwallaye uku.

Messi ya cancanci lashe kofin duniya – Pele

Argentina ta ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida inda ta lashe kofin.

Dan wasan mai shekaru 35 a duniya har sau bakwai Ballon d’Or ya karbi kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa ta Golden Ball bayan da ya zura kwallaye bakwai a raga, yayin da kuma ya zama dan wasa na farko da ya ci kwallo a kowane zagaye na gaba tun bayan da aka fadada gasar zuwa kungiyoyi 32. .

A sakonsa na taya murna a shafinsa na Twitter, Ronaldo, tauraron dan kwallon Brazil a gasar cin kofin duniya ta 2002, ya bayyana kyaftin din Argentina a matsayin ‘haziki.

“Kwallon kafa irin wannan yana kawar da duk wata hamayya. Na ga ‘yan kasar Brazil da dama, da kuma jama’a daga ko’ina cikin duniya, suna taya Messi murna a wannan wasan karshe mai ban mamaki,” Ronaldo ya rubuta a shafin Twitter.

“Wani bankwana da ya dace da gwanin, fiye da zama tauraron gasar cin kofin duniya, ya jagoranci wani zamani. Ina taya Messi murna!