Kotu ta yankewa Malam Abduljabbar hukunci bisa laifin yin sabo

0
106

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano mai zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano, ta samu wani Malami mai suna Abduljabbar Nasiru Kabara da ake tuhumarsa da aikata sabo.

Alkalin kotun, Malam Ibrahim Sarki Yola ya yanke hukuncin ne a zaman kotun da ya dauki sama da sa’o’i biyu. Kafin ya yanke hukuncin, alkalin ya ce, “Na tabbata cewa lauyoyin masu gabatar da kara sun yi nasu bangaren kuma sun tabbatar da hujjojin nasu ba tare da wata shakka ba.

Daga nan kuma ya yanke wa wanda ake tuhuma da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

An dai gurfanar da Abduljabbar a gaban shari’a kan lamarin da ya shafi kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW), matakin da ke iya tada zaune tsaye, a watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da shi.

Har sai da alkali ya furta kalaman nasa na karshe, ya fuskanci Abduljabbar, wanda ya gurfana a gaban kotu domin yanke hukunci na karshe a shari’ar da aka yi masa na tsawon watanni 15, ya nutsu kamar yadda ya saba.