Cristiano Ronaldo ya koma atisaye a Real Madrid

0
111

Cristiano Ronaldo na amfani da filin atisayen kungiyar Real Madrid domin motsa jiki, bayan fitar da Portugal daga gasar cin kofin duniya.

Bayan kawo karshen kwantiraginsa a Manchester United a watan da ya gabata, Ronaldo yana da ‘yancin komawa wani kulob a ranar 1 ga Janairu.

Kungiyar Al-Nassr ta Saudi Arabiya ta yi tayin makudan kudade don siyan dan wasan mai shekaru 37, kodayake an fahimci yana da wasu zabin.

Ronaldo ya yi atisaye shi kadai a sansanin Real Valdebebas kuma babu zabin komawa kungiyar ta Spaniya.

Hukumar kwallon kafar Portugal ta musanta cewa Ronaldo ya yi barazanar ficewa daga kungiyar bayan an gaya masa cewa ba zai fara wasan zagaye na 16 da Switzerland ba, kuma wanda ya maye gurbinsa Goncalo Ramos ya ci kwallaye uku a wasan da suka ci 6-1.

Gasar da aka yi a Qatar ana sa ran za ta kasance dama ta karshe da Ronaldo zai samu na lashe gasar cin kofin duniya, kuma ya fito daga benci a karawar da suka yi da Switzerland da Morocco amma ya kasa hana kasar da ta fito daga yankin Afirka fitar da Portugal.

Dan wasan dai ya nemi shugabannin Real Madrid din su bashi dama ya yi atisaye a filin wasanta, wanda tuni Fiorentina Perez ya amince da bukatar tashi.

Sai dai kuma ana ganin da wuya dan wasan ya koma kungiyar, wadda Ronaldo ya fi kowa zura mata kwallaye a tarihi a wasanni 438 da kwallo 450, inda ya lashe gasar zakarun Turai sau hudu da La Liga sau biyu.

Ronaldo ya koma Real Madrid daga Manchester United a shekara ta 2009 sannan ya koma Juventus a shekarar 2018.