‘Yan sanda sun kama manajan cibiyar ICT JAMB da satar kwamfutoci 83

0
113

Jami’an ‘yan sanda sun kama wani manajan site na Kebna ICT JAMB Centre da ke unguwar Zuru a jihar Kebbi, Abubakar Ismail, bisa laifin satar kwamfutocin cibiyoyin HP guda 83.

Kwamishinan ‘yan sanda, Ahmed Magaji Kontagora, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata, ya ce manajan bayan satar kwamfutocin, ya sayar da su a kan Naira 40,000 kowannensu ga wani Chukwudi Otutu na Cibiyar Kwamfuta ta Otutu da ke Sakkwato.

Ya ce manajan cibiyar, Dr Michael Ezra Dikki, ya bayar da rahoto a hedkwatar ‘yan sanda da ke Zuru cewa, a lokacin da ya kai ziyara, ya gano cewa wanda ake zargin ya sace na’urar tafi da gidanka 83 na cibiyoyin.

“Bayan karbar korafin, tawagar ‘yan sanda ta dauki matakin damke wanda ake zargin tare da kwato guda 76 na kwamfutocin da aka sace,” in ji CP.

Ya ce ‘yan sanda sun fara bincike kan lamarin kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wanda ake zargin.