Kungiyar kabilar Igbo tana zargin INEC da samar da dakin magudin zabe

0
117

Ohanaeze Ndigbo ta zargi INEC da duk wani magudin da suke fuskanta daga ‘yan siyasa, inda ta ce sun daina bude baki ne don magudin.

Kungiyar koli ta zamantakewa da al’adun kabilar Ibo ta ce abin takaici ne  ace hukumar ta INEC ba za ta iya samar da tsaro mai tsafta ga muhimman kayayyakin ta ba.

“Ya kamata su zama masu gudanarwa. Ya kamata su tsara yadda za a gudanar da zabe, kuma hukumar da ya kamata ta tsara zabukan ta na korafi. Ina zamu je?

Ya kamata a samar da hanyar da za a tabbatar da cewa abubuwa suna aiki daidai.

“Ya kamata mu yi musu korafi amma yanzu su ne suka kawo mana korafi.

“Dole ne a bude, shi ya sa wasu daga cikin wadannan abubuwan ke faruwa.

“Idan da gaske akwai samfurin lantarki da suke ƙoƙarin amfani da su, ba shakka waɗannan abubuwan ba za su faru ba.

“Hakan na daga cikin matsalolin rashin samar da hanyoyin da suka dace don gujewa duk wadannan kura-kurai.

“Abin da suke yi kenan, abin da suka dade a INEC har zuwa yanzu, kuma idan da duk wata dama da kudi da aka ba su, ba za su iya tabbatar da sahihin zabe da kauce wa magudi ba; abin takaici ne,” in ji Sakataren Yada Labarai na Ohanaeze Ndigbo, Dokta Alex Chidozie Ogbonnia.