Shekau ya mutu ya bar kwarkwara 83 – Tsoffin Kwamandodin Boko Haram

0
111

Wasu Tsoffin Kwamandodin Boko Haram sun sanar da cewar shugabansu Abubakar Shekau ya mutu ya bar kwarkwara 83, lokacin da ya bar duniya.

Mai bai wa Gwamnan Jihar Borno shawara a kan harkokin tsaro, Janar Abdullahi Ishaq ya sanar da wannan labari, yayin da ya bayyana cewar wasu tubabbun kwamandodin Boko Haram da suka aje makamansu ne suka shaida masa.

Janar Ishaq ya ce lokacin da suka karbi wasu daga cikin tubabbun a garin Bama ne daya daga cikinsu ya fara shaida masa wannan labari na cewar Shekau ya bar mata 83 wadanda babu aure a tsakaninsu, amma suna zama da shi a matsayin kwarkwara.

Mai bada shawarar yace tubabbun kwamandan sun shaida masa cewar yanzu haka Shekau na wutar jahannama saboda yadda ya hallaka kansa sakamakon arangamar da suka yi da kungiyar da basa ga maciji da juna ta ISWAP.

Janar Ishaq ya ce tsohon shugaban na basu kwarin gwiwar fita domin zuwa yaki, yayin da ya ke tabbatar musu cewar idan sun mutu a fagen daga, tarin ‘yan mata na jiransu a Aljannah.

 

RFI