Bidiyon Dala: Ganduje da Jaafar Jaafar sun hadu a London

0
106

Dan jaridar nan da ya fitar da bidiyon zargin Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano da karbarĀ  daloli a matsayin cin hanci, Jaafar Jaafar ya hadu gwamnan a kasar waje.

A ranar Litinin Jaafar Jaafar, mawallafin jaridar Daily Nigerian, ya wallafa bidiyon haduwarsu da Ganduje a birnin London na kasar Birtaniya.

Duk da takaddamar da ke tsakaninsu, a karon farko, a bidiyon, an ga Gwamnan Ganduje da Jaafar Jaafar kowannensu cikin sakin fuska da raha, suka sha hannu, sannan suka rungume juna.

Hakan ta kasance ne a harabar Chatham House, inda dan takarar shugaban kasa na Jamā€™iyyar APC, Bola Tinubu ya je gabatar da jawabi a ranar.