Majalisar dokokin kasar Peru ta tsige shugaban kasar

0
106
Majalisar Dokokin Kasar Peru ta tsige Pedro Castillo daga Shugabancin Kasar don ya fuskanci shari’a.

’Yan Majalisar dai sun amince da tsige shin ne da kuri’a 101 ta goyon baya, sai guda shida da suka nuna rashin amincewa, daya kuma bai halarci zaman ba.

Sun kuma umarci Mataimakinsa, Dina Boluarte, da ya karbi ragamar mulkin kasar.

Matakin dai na zuwa ne jim kadan bayan tsohon Shugaban ya bayyana aniyarsa ta yunkurin rushe majalisar na wucin gadi don ya ci gaba da mulki da dokokin sojoji sannan ya shirya sabon zabe.

Tuni dai sojojin kasar suka gargadi tsohon Shugaban da kada ya kuskura ya yi wa Kundin Tsarin Mulkin Kasar karan tsaye.

’Yan majalisar dai sun ce Shugaban zai iya rushe majalisar ce kawai idan an jefa kuri’ar yanke kauna har sau biyu a kanta. Sun ce duk wani yunkuri na yin akasin haka ya saba wa kundin mulki kasar.