Reuters sun zargi sojojin Najeriya da zubar da cikin mata sama da 10,000 a Borno

0
102

Wani bincike da kamfanin dillancin labaran Reuters yayi a Najeriya ya zargi sojojin kasar da mallakar cibiyoyin zubar da cikin mata a Jihar Borno, wanda ake amfani da su a asirce wajen zubar da cikin mata sama da 10,000 da suka samu ciki daga mayakan Boko haram.

Wani rahoto na musamman da Reuters ya gabatar yace tun daga shekarar 2013 aka kaddamar da aikin, kuma sojojin sun zubar da cikin akalla mata da yan mata 10,000 a asirce, kamar yadda wasu daga cikin su suka shaida masa.

Reuters yace ana zubar da cikin wadannan mata ne ba tare da saninsu ba, wajen yi musu allura ko kuma basu magunguna kamar yadda 33 daga cikin matan da aka zubarwa cikin suka shaida masa anyi musu, lokacin da suke tsare a hannun sojojin.

Wadannan matan sun shaidawa Reuters cewar wasu daga cikin wuraren da ake amfani da su wajen zubar da cikin sun hada da Barikin Giwa da Barikin Maimalari da kuma wasu asibitocin fararen hula guda 2 da suka hada da asibitin kwararru da kuma asibitin Umaru Shehu dake Maiduguri.

Binciken yace yadda ake aikin na tattare da sarkakiya, ta yadda wasu daga cikin ma’aikatan asibitin da ake zubar da cikin ma basu san abinda ke faruwa ba.

Wasu daga cikin matan da suka ce an zubar musu da cikin, sun yi zargin cewar bada san ransu akayi ba, kamar yadda Yagana Bukar ta shaidawa Reuters, inda take cewa da tana da zabi, da ta zabi goya ‘danta, yayin da wasu kuma suka yi zargin cewar mata da dama sun rasa rayukansu sakamakon hanyoyin da ake amfani da su wajen zubar da cikin.

Sai dai manyan jami’an sojojin Najeriya sun yi watsi da wannan zargi, cikinsu harda kwamandan rundunar sojin dake yaki da boko haram, Manjo Janar Christopher Musa, wanda ya zargi Reuters da yunkurin yiwa yaki da ‘yan ta’adda zagon kasa.

Janar Musa yace atafau wannan abin baya faruwa a Najeriya, saboda yadda suke mutunta rayukan mata da kuma yara kanana.

Laftanar Janar Lucky Irabor, Hafsan hafsoshin Najeriya da shugaban rundunar sojin kasa, Laftanar Janar Faruk Yahya basu mayar da martani akan rahotan ba, amma Daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Jimmy Akpor ya bayyana rahotan na Reuters a matsayin wani mugunta da cin zarafi ga al’ummar Najeriya.

Janar Akpor yace an horar da sojojin Najeriya ta hanyar da ta dace wajen kare lafiyar jama’a da kuma sadaukar da rayukansu, musamman wajen kare lafiyar mata da yara da kuma tsofaffi, saboda haka babu dalilin daukar irin wannan mataki na zubar musu da ciki.

Sai dai Reuters yace wasu jami’an kula da lafiya guda 4 da suka yi magana da shi, sun shaida masa cewar ana gudanar da shirin zubar da cikin ne domin kare lafiyar matan da yaran da zasu haifa, saboda karda su fuskanci tsangwama sakamakon fitowa a matsayin ‘yayan yan ta’adda.

Reuters yace ya tuntubi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, lura da cewar tun a lokacin sa aka fara aikin zubar da cikin, amma sai kakin sa yace tsohon shugaban bashi da masaniya akai, yayin da ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ma’aikatar tsaron kasa dake Abuja da Cibiyar rundunar sojin Najeriya da kuma Runduna ta 7 dake Maiduguri suka ki cewa uffan dangane da zargin.

Kamfanin dillancin labaran ya kuma ce shima tsohon hafsan hafsoshin sojin kasa a Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai bai ce komai ba dangane da rahotan, yayin da sojojin da suka yi magana da Reuters suka ce suna samun umarni ne daga manyan su akan yadda ake aikin cikin sirri da kuma yadda ake binne matan da suka mutu idan an samu kuskure.