Kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudiyya ta yi wa Ronaldo gagarumin tayi

0
109

Kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudiyya ta yi wani gagarumin tayi na sayen dan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo bayan kammala gasar cin kofin duniya.

Kungiyoyin da dama sun nuna sha’awarsu kan dan wasan, inda Al-Nassr ta yi tayi mafi girma a kan kudi kusan Euro miliyan 200 a shekara, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Ronaldo mai shekaru 37, baya tare da wata kungiya a halin yanzu, bayan raba gari da tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United a watan jiya, biyo bayan wata hira da aka yi da shi mai cike da cece-kuce.

A cikin hirar da ya yi da TalkTV, ya ce ya ki amincewa da yarjejeniyar da aka kulla na sama da Yuro miliyan 305 don shiga wani kulob na Saudiyya, matakin da zai sa ya zama dan wasan kwallon kafa mafi tsada a duniya.

An fahimci cewa Ronaldo ya jajirce sosai a gasar cin kofin duniya ga kasar sa Portugal kuma har yanzu ana dakon abin da ya yanke game da makomar sa bayan kammala gasar da ke gudana a Qatar.

Portugal zata fafata da Switzerland a zagayen ‘yan 16 a Qatar ranar Talata.

Tun da farko a gasar, Ronaldo ya zama dan wasa na farko da ya zura kwallo a gasar cin kofin duniya sau biyar, bayan da ya zura bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da suka doke Ghana da ci 3-2.

Duk da cewa shi dan wasa ne da baya tare da wata kungiya, Ronaldo ba zai iya sanya hannu a sabon kulob ba har sai ranar 1 ga watan Janairu saboda ya kulla da United a lokacin da aka rufe kasuwar musayar ‘yan wasa ta karshe.

Har ila yau, dole ne ya dakatar da buga wasanni biyu a matakin gida da kowane sabon kulob a Ingila ko kuma a waje, saboda samun sa da laifin hankade waya daga hannun wani dan kallo a wasan da United ta kara da Everton a kakar wasa ta bara.

Ronaldo ya ci kwallaye 145 a wasanni 346 da ya buga wa United sama da shekaru biyu, inda ya bar Real Madrid a shekarar 2009 kafin ya koma Old Trafford daga Juventus a 2021.