Mutum 6 sun mutu bayan cin abinci da ake zargin tsaka ta saka baki

0
106

Wasu ƴan gida ɗaya su shida sun mutu bayan da aka ce sun ci abinci da ake zargin tsaka ce ta sa baki a unguwar Mowe da ke karamar hukumar Obafemi Owode a jihar Ogun.

Wadanda su ka rasun, da su ka haɗa da Adeleke John Samuel, wani akawun hayar, matarsa, Pamela Adeleke, ‘ya’yansu biyu da wasu ‘yan uwansu biyu, an gano gawarwakinsu ne da sanyin safiyar Juma’a, kamar yadda rahoton jaridar TheEagle Online ya bayyana.

Rahoton ya kara da cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Lawal Ojo, mai gadin gidan ya yi zargin akwai wata matsala bayan da ya ji gidan ya yi tsit da safe ba kamar yadda aka saba jin hayaniya ba.

“Ya sanar da makwabtansu, inda su ka kutsa cikin gidan sai kawai suka ga gawarwakinsu a dakuna daban-daban,” in ji rahoton.

“Dukkan su suna cikin yanayin barci, in ji majiyar, wanda ke nuni da cewa watakila sun mutu a cikin barcinsu.”

A cewar rahoton, Ifenatuora Ijeoma, wacce ta shaida lamarin, ta ce mai yiwuwa sun ci gubar ne a lokacin da su ka ci abincin dare.

Ta tabbatar da cewa, bayan da aka duba kayan kicin din, an ga wata matacciyar tsaka a cikin tukunyar miya.