Qatar 2022: Marocco ta kasance kasar Afirka ta farko da ta jagoranci rukuni

0
121

Morocco ta zama kasa ta biyu a Afirka, inda ta biyo bayan Senegal daga Afirka zuwa zagaye na gaba a gasar ta cin kofin duniya.

Shekaru hudu kenan da gazawar kasashen Afirka tsallakawa zagayen ‘yan 16 a gasar da aka fafata a kasar Rasha da aka yi a 2018.

Sai dai abin tambayar shine, ko kasashen Afirka da suka samu nasarar zuwa zagayen na gaba za su iya tsallakawa zagayen wasan dab da na kusa da karshe?

Marocco dai ta kasance jagora a rukunin F da ya kunshi kasashen Croatia, Belgium da Canada.

Yanzu haka dai kasashen Kamaru da Ghana suka rage a rukuni a gasar da ke gudana a kasar Qatar.