Amurka da Faransa na duba yadda za a magance matsalolin da suka addabi duniya

0
94

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya samu tarba ta ban girma daga fadar shugaban kasar Amurka Joe Biden, a wata ziyarar karfafa alakar da ke tsakanin kasashen bayan rikicin kasuwancin jirgin yakin Australia da ya kunno kai tsakanin kasashen biyu.

Bayan bikin tarbar shugaba Macron din, shugabannin biyu sun kuma kebe a Ofishin Oval don fara tattaunawa kan batun yakin na Ukraine, da kuma yadda turai zata tunkari China, da kuma matsin tattalin arziki da duniya ke fama da shi.

Bayan tattaunawar, shugabannin biyu ana sa ran zasu kuma tattauna da manema labarai, kafin daga bisani su jagoranci wata liyafar cin abinci.

Ziyarar dai ta nuna yadda kasashen biyu suka yafewa juna game da rikicin da ya so tashi a tsakanin su a bara, la’akari da yadda Faransa ta zargi Amurka da kwace cinikin kera jiragen yaki da ta kulla da Australia.