’Yan bindiga sun kashe mutum 7, sun sace 5 a sabon hari a Sakkwato

0
94

Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum bakwai tare da yin garkuwa da wasu biyar a wasu sabbin hare-hare a kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni a Jihar Sakkwato.

Maharan sun kashe mutum shida a kauyen Bare, daya kuma a Kagara, suka sace mutum biyar, ciki har da wani magidanci da matansa biyu a kauyen Faji, sannan suka wawushe kaya da ba a san iyakarsu ba a shagunan jama’a.

Yankunan da aka kai wa harin sun hada da, Bare, Kagara, Kojiyo a Karamar Hukumar Goronyo da kuma kauyen Faji a Karamar Hukumar Sabon Birni.

Da yake tabbatar da harin, Shugaban Karamar Hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, ya ce ’yan bindigar sun yi awon gaba wasu mutum biyar da dabbobi a kauyukan.

A cewarsa, an kai harin ne a ranar Laraba da yamma.

Da aka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, DSP Sanusi Abubakar, amma ya ce ba shi da labari, amma ya yi alkawarin samun cikakken bayani.