Samun man fetur ne ya kashe masana’antunmu – Al-Mustapha

0
98

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha ya bayyana ce-wa samun man fetur ne ya yi sanadiyyar kashe manyan masana’antun Najeriya.

Al-Mustapha ya bayyana hakan ne a Abuja lokacin da yake jawabi a wurin taron ilimi karo na 34 da kungiyar ma’aikata masu sarrafa auduga da dinkawa (NUT-GTWN) suka shirya tare da hadin gwiwar kungiyar kwadugo (NLC).

A cewar Al-Mustapha, samun danyan mai a shakarun 1970 ya yi makasudin ya-waitar rashin ayyukan yi sakamakon dunkushewar masana’antun auduga da ake da su a baya.

Dan takarar shugaban kasan ya kara da cewa an san da cewa samun man fetur yana da matukar muhummanci ga kasar nan wajen kara samar da kudaden shiga domin taimaka wa masana’antu, amma a bangare daya kuma ya durkusar da masana’antun auduga da sauran kamfanoni.

Ya ce lokacin da aka gano danyan mai, Najeriya ta fara samar da manyan kayayya-ki na gida, amma lokacin da aka cakuda siyasa a cikin lamarin, sai aka fara samun matsala.

Al-Mustapha ya ce, “Su wadanda suka fara amfani da kudaden shiga daga man fe-tur, sai suka amince da mummunan tsarin siyasa na kasa da kasa, inda suka ci gaba da dibar man daga wannan tsarin har sai da suka kashe sauran fannonin samun kudaden shiga na kasa.”

Dan takarar shugaban kasan ya yi kira ga shugabanni da su yi karatun ta-natsu tare da yin tunanin abubuwan da kasar nan take bukata.