Sanata Barau ya ba ’yan wasan kwallon hannu ta Kano Pillars kyautar N2m

0
94

Dan majalisar dattijai mai wakiltar Kano ta Arewa Sanata Barau I. Jibrin ya ba ’yan kungiyar wasan kwallon hannu na Kano Pillars da kuma ta mata Safety Babes, kyautar Naira Miliyan biyu.

Sanatan ya basu kyautar ne a bisa nasarar da su ka samu na lashe gasar cin kofin ‘Prudent Energy’ wanda aka gudanar a jihar Legas a farkon watan Nuwamba.

Sanatan ya mika kyautar kudin ne lakadan ga Shugaban Hukumar Kula da Wasanni ta Jihar Kano, Ibrahim Galadima, a wani dan kwarya-kwaryar biki a ofishinsa a ranar Alhamis.

A jawabinsa yayin karbar kudin, Ibrahim Galadima ya yi godiya tare da jinjina wa Sanata Barau Jibrin bisa wannan karimci, da kuma cika alkawarin bayar da wannan kudin da ya yi a gaban gwamna.

A jawabin hadimin sanatan mai kula da tallafi da karfafar matasa, Hafizu Sani Liman Kofar Mata, wanda ya kai sakon kudin,  ya kawo kudin ne a bisa alkawarin kyautar da sanatan ya yi.

Sanatan ya yi alkawarin ba wa kungiyar kwallon hannun kyautar kudin ne a wani taron gabatar da ’yan wasan da kuma kofin da au ka ci ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.