Gwamnati ta dauki malaman darasin tarihi 3,700

0
121

Gwamnatin Tarayya ta dawo da darasin tarihi a makarantun firamare da sakandare bayan shekara 13 da sokewa.

A halin yanzu gwamnatin ta dauki malaman bangaren guda 3,700 domin ba su horo da nufin inganta koyar da darasin a shekarar 2009/20210.

Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimi a Matakin Farko (UBEC), Hamid ya ce an dauki malaman ne a jihohi 36 da Birnin Tarayya, inda a kowace jiha aka dauki mutum 100.

Da yake jawabi a taron kaddamar dawo da darasin da kuma horas da malaman, Ministan Ilimi Adamu Adamu ya ce dakatar da darasin da aka yi a baya ya haifar da karuwar lalacewar tarbiyya da raya al’adu.

Adamu Adamu, ya bayyana haka ne ta bakin Minista a Ma’aikatar Ilimi, Goodluck Opiah, a taron, wanda ya wakilce shi a taron da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta.

A jawabinsa, Sarkin Musulmi, ya yi kira ga sarakunan gargajiya da sauran ’yan Najeriya da su taimaka tare da goyon bayan  gwamnatin kan dawo da darasin tarihi a makarantun firamare da sakandare.