Qatar 2022: Iran ta lallasa Wales da ci 2

0
109

Kasar Iran ta lallasa Wales da ci 2 da babu a Gasar Cin Kofin da ake yi a Kasar Qatar na 2022.

Dragons dai na da burin ganin an samu ci gaba da ci 1-1 da Amurka a wasansu na farko a ranar Litinin, amma sun yi kokarin samun nasara a kan Iran da ta samu zakudawa gaba, inda suka ga mai tsaron gida Wayne Hennessey ya kori a saura minti hudu a tashi daga wasan.

Rouzbeh Cheshmi da Ramin Rezaeian ne suka samu zura kwallayen a lokacin da aka cire musu tsammanin samun nasara.

Wales ta yi ta fafatawa da yin iya kokarinta domin ganin ta samu tsira a zagayen gasar bayan dawowa daga hutun rabin zango a kan Iran amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba domin a karshe sun amshi kwallaye 2 daga wajen Iran din.

Wales dai a yanzu tana da dama na karshe da ta karawa da kasar England a zagayen na karshe da zai gudana a ranar Talata.