Matsalar karancin mai ta ta’azzara a Lagos

0
110

Matsalar karancin man fetur ta karade sassan birnin Lagos da ke kudancin kasarnan, yayin da al’umma ke nuna damuwa kan musabbabin karancin duk da cewa,  ‘yan kasuwa masu zaman kansu na sayar da lita guda sama da Naira 210

A halin yanzu, daidaikun gidajen mai ne ke sayar da fetur din a sassan jihar ta Lagos, yayin da dama ke ci gaba da kasancewa a rufe.

Wakilan RFI Hausa sun bada rahoton yadda motoci da babura suka yi dogayen layuka a kokarinsu na ganin sun sayi man.

Wasu daga cikin gidajen man na sayar da lita guda akan farashin Naira 210 ko 215 zuwa 220, sabanin farashin da gwamnati ta kayyade na Naira 169 zuwa 170.