Qatar 2022: Har yanzun ba kasar Afirka da ta zura kwallo ko daya a raga

0
116

A ranar 20 ga watan Nuwamba 2023 aka soma gasar cin kofin duniya ta bana a kasar Qatar, inda har yanzun kasashen Afirka ke fama da kokarin zura kwallo a raga.

A ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamba, Senegal ta sha kashi a hannun kasar Netherlands da ci 0:2 yayin da kasar Morocco ta tashi kunnan doki da kasar Croatia 0:0 a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba.

Kasar Qatar mai masaukin baki kuma, a wani bangare ta sha kashi a hannun kasar Ecuador da ci 0:2 yayin da kasar Saudia ta samu nasara mai ban mamaki yayin da ta doke kasar Argentina da ci 1:2.