Bayan sauke daraktan NYSC, Christy za ta rike mukamin na wucin gadi

0
128

Biyo bayan sauke Birgediya-Janar Muhammad Kaku Fadah daga mukaminsa na darakta janar na Hukumar Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC), daraktar sashen Kimiyya da Fasaha, Christy Uba, za ta rike mukamin na wucin gadi.

A makon da ya wuce ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya cire Fadah daga kan mukamin.

Buhari a ranar 17 ga watan Nuwambar 2022 ne, ya amince da a cire Fadah daga kan mukamin.

Rahotannin sun ce, shugaban ya bayar da umarnin a cire Fadah ne, saboda gazawarsa na iya tafiyar da hukumar.

A cikin wata sanarwar da kakakin hukumar ya fitar, ta ce ganin cewa, Christy ita ce babba yanzu a hukumar shi ya sa shugaban kasa ya amince da ta rike mukakin na wucin gadi kafin a nada wani sabon shugaban.