Manchester United ta sallami Cristiano Ronaldo

0
127

Dan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo zai bar kulob din Manchester United ba tare da wani bata lokaci ba.

Hakan ya biyo bayan wata hira da ya yi wadda ta jawo takaddama, inda dan wasan mai shekara 37 ya soki kungiyar har da cewar baya martaba cochinta Erik ten Hag.

United da wakilan Ronaldo duk sun tabbatar da raba gari a tsakaninsu.