Najeriya za ta sami gangar man fetur biliyan daya daga Rijiyar Man Kolmani – NNPCL

0
106

Yayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke dab da kaddamar da fara hakar man fetur a rijiyar Kolmani da ke tsakanin jihohin Gombe da Bauchi, Najeriya za ta sami gangar man kimanin biliyan daya a wajen.

Kazalika, kasar za ta sami sama kyubic mita biliyan 500 na iskar gas daga rijiyar ta farko da aka gano a yankin.

Ana kuma hasashen adadin na iya kai wa ganga biliyan 19 idan aka kara samun wasu rijiyoyin a nan gaba.

Wasu bayanai da Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya wallafa a jerin shirye-shiryen bude hakar man na ranar Talata ne suka tabbatar da hakan.

NNPCL ya kuma ce, “Kashin farko na aikin zai kunshi kafa matatar mai mai karfin tace ganga 120,000 a kowace rana, matatar sarrafa iskar gas da za ta iya tace kyubik mita miliyan 500.

“Za kuma a kafa tasar da za ta samar da megawat 300 na wutar lantarki da kuma masana’antar sarrafa takin zamanin da zai kai tan 2,500 a kullum.”

Wannan dai shi ne karo na biyu da Shugaba Buhari zai ziyarci wajen, inda ko a watan Fabrairun 2021 ya je domin kaddamar da fara hakan.

Kamfanin na NNPCL ya ce an fara binciken man a yankin ne tun a shekarun 1990, kuma aka damka aikin a hannun kamfanonin Shell da Chevron, amma suka yi watsi da shi.

A baya dai kamfanonin sun yi korafin cewa yankin tsandauri ne babu ruwa, lamarin da ya sa zai yi musu wahala su yi jigilar man don fitar da shi waje.