Qatar 2022: Fitattun ‘yan wasa 10 da suka koma ‘yan kallo

0
130

Tun a watanni biyu zuwa uku baya ’yan wasa da dama suka fara kaffa-kaffa domin guje wa jin rauni da zai hana su samun damar zuwa gasar, wadda take cikin manyan burukan duk wani dan kwallon duniya.

Sai dai duk da hakan, wasu sun ji raunuka da za su hana su, inda wasu daga cikinsu ma sun ji raunin ne bayan kasarsu ta sanya sunansu a cikin ’yan wasanta.

Aminiya ta tattaro wasu fitattun ’yan wasa da ba za a ga fuskokinsu ba a gasar ta bana, ko dai saboda rauni ko kuma kasarsu ba ta samu zuwa ba.

1. Karim Benzema

Benzema shi ne Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Duniya na yanzu.

Kusan za a iya cewa da shi kasarsa ta Faransa ke tutiya a yanzu, musamman ganin yadda ya dauki kungiyarsa ta Real Madrid a kakar bara zuwa bana.

Wasu daga cikin magoya bayan Real Madrid sun zargi Benzema da kin buga wasu wasannin kungiyar domin guje wa samun rauni.

Sai dai duk da hakan, bayan Faransa ta sa sunan dan wasan, har sun sauka a kasar Qatar, sai ya ji rauni a atisaye, sannan bayan gwaji aka tabbatar ba zai buga gasar ba.

Watakila shi ke nan Benzema ya yi ban-kwana da gasar Kofin Duniya har abada.

2. Sadio Mane

Dan wasan kasar Senegal, Sadio Mane, ne ya zo na biyu a bikin Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Duniya kuma shi ne Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Afirka.

Shi ne babban dan wasan kasar Senegal a yanzu, da a iya cewa masoya kwallon kafa a yankin Afirka suka so gani a gasar.

Dan wasan ya ji rauni ne a wani wasan kungiyarsa Bayern Munich, inda bayan gwajin farko aka ce zai buga wasu wasannin, amma daga baya, bayan sun sauka a kasar Qatar aka sake gwaji, aka tabbatar cewa ba zai buga gasar ba.

3. Erling Haaland

Matashin dan kwallon da za a iya cewa yanzu tauraronsa ya fi haskawa.

Zuwansa kungiyar Manchester City a farkon kakar bana ya daga hankalin duniya.

Amma sai sai dai kash! Kasarsa ta Norway ba za ta buga gasar ba.

4. David De Gea

De Gea golan Manchester United da kasar Spain ne, kuma ya dade yana jan zarensa, musamman a Manchester United da aka tabbatar yana cikin masu taimakon kungiyar.

Sai dai shi ba kaman sauran ba da rauni ya hana, shi baki daya ma ko gayyatarsa ba a yi ba, wanda hakan ya sa wasu mamaki.

5. Mohammad Salah

Fitaccen dan wasan kasar Masar da kungiyar Liverpool, Mohammad Salah za a yi kewarsa ne saboda kasarsa ta Masar ba ta samu gurbin shiga gasar ta bana ba.

6. Paul Pogba

Paul Pogba ya dade yana fama da raunuka.

A watan Satumba ne aka yi wa dan wasan tiyata a kafa, aka yi tunanin cewa zai warke kafin lokacin gasar, amma bai warke ba har zuwa yanzu.

Hakan ya sa  za a ji kewarsa a gasar ta bana.

7. Jado Sancho

Matashin dan wasan kasar Birtaniya da kungiyar Manchester United.

Sancho za a iya cewa ya yi faduwar tasa; Daga wanda aka sayo a sama da Fam miliyan 70, zuwa wanda aka gayyata zuwa Gasar Cin Kofin Duniya.

Kasarsa ta Ingila ba ta gayyace shi ba ne shi ma baki daya.

8. Roberto Firminho

Roberto Firminho dan wasan kasar Brazil ne da kungiyar Liverpool.

Dan wasan gaba ne da ke nuna kwarewa matuka, amma kasar Brazil ba ta gayyace shi ba baki daya.

9. Kante

Kante dan wasan tsakiyar kungiyar Chelsea ne da kasar Faransa.

Dan wasan ya samu rauni ne da dadewa, kuma bai warke ba har zuwa yanzu.

10. David Alaba

Alaba dan asalin Najeriya ne da yake wakiltar kasar Austria a yanzu da kungiyar Real Madrid.

Shi ma kasarsa ce ba za ta samu zuwa gasar ba, bayan kasar Chile ta doke su a wasan raba-gardama.